Venezuela

Nicolas Maduro ya lashe zaben shugaban kasar Venezuela

Zababben shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro
Zababben shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro REUTERS/Tomas Bravo

Shugaban rikon kwaryar gwamnatin kasar Venezuela, Nicolas Maduro ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a jiya Lahadi da rinjaye mara yawa, inda aka bayyana shi a matsayin sabon shugaban kasar bayan mutuwar tsohon shugaban kasar, Hugo Chavez. 

Talla

Maduro, a cewar hukumar zaben kasar ta Venezuela, ya samu nasarar lashe zaben ne da kashi 50.7 a yayin da abokin hamayyarsa kuma gwamnan Jihar Miranda, Henrique Capriles ya samu kashi 49.1 na kuri’un da aka kada.

Hukumar zaben kasar har ila yau ta bayyana cewa an riga an kidaya fiye da kashi 99 na kuri’un da aka kada.

Maduro dan jam’iyar Socialist, tun a lokacin yakin neman zabe ya bayyana aniyarsa ta cigaba da dora ayyukan da zai yi ma kasar akan manufofin da Chavez ya fara kan mutuwarsa.

Sai dai Capriles, dan shekaru 40 ya ce bai amince da sakamakon zaben ba, duk da rahotanni dake nuna cewa ya gana da Maduro ta wayar talho jim kadan bayan an sanar da sakamkon zaben.

An dai haifi Nicolas Maduro ne a ranar 23 ga watan Nuwamba a shekarar 1962 ya kuma fito ne daga rukunin marasa galihu, inda ya halarci makarantar Firamari mallakar gwamnati.

A da Maduro ya kasance matukin motar sufuri ne kirar bas, inda daga bisani ya zama daya daga cikin shugabannin ‘Yan kwadago a kasar ta Venezuela.

An fara zaben Maduro ne a matsayin dan majalisar kasar a shekarar 2000, ya kuma taba zama Kakakin majalisar kasar ta Venezuela a tsakanin shekarun 2005 da 2006.

Kana ya kuma rike mukamin Ministan harkokin wajen kasar tun daga shekarar ta 2006, mukamin da aka hada mai ya rike da na mataimakin shugaban kasar har izuwa lakacin da ya zama shugaban gwamnatin rikon kwarya bayan mutuwar Chavez a watan Maris.

Mutane da dama na ma maduro kallon dan gani kashe nin Chavez inda ake cewa akwai kyakyawar dangantaka tsakaninsu baya ya ga ta siyasa.

A kuma ranar 8 ga watan Disambar bara ne Chavez ya zabe shi a matsayin wanda zai maye gurbinsaa lokacin da zai tafi neman magani a Cuba.

Maduro dai na da mata guda daya wacce ake kira Celia Flores, wacce itama fitacciyar ‘Yar siyasa ce.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI