Korea-Amurka

Korea ta Arewa ta gindaya sharrudan hawa teburin tattaunawa

Shugaban Korea ta Arewa, Kim Jong-un
Shugaban Korea ta Arewa, Kim Jong-un

Kasar Korea ta Arewa, ta gindaya wasu sharadodi da take bukata kasar Amurka da Korea ta Kudu su cimma, kafin ta zauna teburin tattaunawa da kasashen kan shirin ta na makamin nukiliya.

Talla

Wadannan sharadodi da ake ganin suna da wuya Amurka da Korea ta Kudu su amince da su, sun hada da cire daukacin takunkumin da aka kakabawa kasar a zauren Majalisar Dinkin Duniya, da kuma kawo karshen atisayen soji da ake tsakanin Amurka da Korea ta kudu.

An bayyana matsayin Korea ta Arewan ne a wata sanarwa da Hukumar tsaron kasar ta bayar, wanda aka yada a kafar yada labaran Gwamnati.

Sanawar ta ce, muddin Amurka da abokiyar gabar kasar, wato Korea ta Kudu na neman tattaunawa ta gaskiya, to ga dama sun samu.

Korea ta kuma ce babu yadda za’ayi zaman lafiya muddin Amurka na kada gangar yaki.

Tuni dai Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Korea ta Kudu, Cho Tai young, ya yi watsi da bukatar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI