Kwallon kafa

Tottenham ta doke Manchester City, Liverpool da Chelsea sun ta shi da ci 2-2

Sabon kocin Tottenham, Andre Villas- Boas
Sabon kocin Tottenham, Andre Villas- Boas

Manchester City ta sha mamaya a hanun Tottenham Hotspur da ci 3-1 a karawar ad suka jiya Lahadi a fagen gasar Premier, a yayin da wasa tsakanin Liverpool da Chelsea ak tashi da ci 2-2. 

Talla

Arsenal dai ta sake daidaita zamanta a matsayi na uku a saman teburin gasar baya ta doke Fulham da ci 1-0, a yayin da Stoke City da Sunderland da Norwich suka samu nasara, wanda hakan ya kara musu kwarin gwiwar ci gaba da kasancewa a cikin gasar ta Premier.

Sunderland dai ta doke Everton ne da ci 1-0, kana Stoke ta lallasa Queen’s Park Rangers da ci 2-0, a yayin da Norwich kuma ta doke Reading da ci 2-1.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI