Syria

Hari ya yi sanadiyar lalata husumiyar tsohon Masallacin Aleppo

Wani masallaci da aka bata a Damascus bayan wani hari
Wani masallaci da aka bata a Damascus bayan wani hari Reuters

Fadan da ake cigaba da gwabzawa a kasar Syria, ya lalata husumiyar Masallacin Aleppo, da aka gina a tun a karni na 11. 

Talla

Ana dai zargin sojin Gwamnati ne da kai hari Masallacin da Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da al’adu, kimiya da ilimi ta sanya shi a cikin kayan tarihin duniya,

Hakan ya sa shugaban ‘Yan Tawayen Syria, Ahmed Moaz al Khatib ya bukaci kungiyar Hezbolah da ta fice daga kasar ko kuma su kai mata hari Lebanon.

Suma bangaren Gwamnati sun zargi ‘Yan adawar da cewa su suka kai hari Masallacin mai dimbin tarihi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI