Bangladesh

Har yanzu ba a ga daruruwan mutane da ginin Bangladesh ya rufta da su ba

Iyalai suna duba sunan 'Yan uwansu da hadarin rutsa da su
Iyalai suna duba sunan 'Yan uwansu da hadarin rutsa da su REUTERS/Stringer

Har yanzu ana kyautata zaton wasu daruruwan mutane sun bace, bayan da wani gini ya rufto musu a ranar Larabar da ta gabata, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 273.

Talla

Rahotanni na nuna cewa jami’an ceto sun zakulo fiye da mutane 40, daga inda lamarin ya faru, a yankin da ake da masaku a kusa da birnin Dhaka.

Firaministan kasar, Sheikh Hasina ya yi kiran a yi addu’a ta musamman ga mamatan, a duk fadin kasar.

A daya bangaren kuma, rahotanni daga Bangladesh na nuna cewa an samu barkewar rikici tsakanin jami'an tsaro da masu zanga zanga a kasar, wadanda suka fito domin su nuna rashin jin dadin game da hadarin, suna masu kira da a hukunta masu laifi a cikin lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI