Wasan Tennis

Nadal ya lashe Barcelona Open, Sharapova ta lashe gasar Porsche Grand Prix

Rafael Nadal (a hagu) da Maria Sharapova (a dama)
Rafael Nadal (a hagu) da Maria Sharapova (a dama) cdn01.cdn.justjared.com

A karo na takwas Rafeal Nadal ya sake lashe kofin gasar Barcelona Open bayan ya doke Nicolas Almagro da ci 6-4 6-3 a wasan karshe. Wannan kuma shine karo na uku da yake lashe gasar a jere.  

Talla

A daya bangaren kuma, Maria Sharapva ta kare kofinta na gasar Porsche Grand Prix bayan ta doke Li Na da ci 6-4, 6-3.

Wannan itace nasara ta biyu da Sharapova, ‘Yar asalin kasar Rasha ke samu a wannan shekara bayan ta lashe kofin Indian Wells.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI