Premier League

Robin Van Persie ya zira kwallo a ragar Arsenal, QPR da Reading sun fice gasar Premier

Dan wasan Manchester United, Robin Van Persie
Dan wasan Manchester United, Robin Van Persie

Manchester United ta tashi kunnen doki da abokiyar abokiyar hamayyarta Arsenal da ci 1-1, a yayin da ita Arsenal ke kokarin mallakar gurbin buga gasar Zakarun Turai a kaka mai zuwa. Kuma Tsohon dan wasan Arsenal, wato Robin Van Parsie ne ya farkewa Manchester kwallo a cikin minti na 29 bayan dan wasan Arsenal Theo Walcott ya yi amfani da wata dama da ta bullo kai bayan Van Persie ya yi wani kuskure.  

Talla

A daya bangaren kuma Reading da Queens Park Rangers sun fice daga rukunin buga gasar Premier bayan sun tashi babu ci ko daya a wasan su.

Da ma dai kungiyoyin kwallon kafan suke karkshin teburin gasar ta Premier inda kowanen su ke da maki 25.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga na nuna cewa, Liverpool ba tare da dan wasanta Luis Suarez ba, ta lallasa Newcastle da ci 6-0, Everton kuwa ta doke Fulham da ci daya mai ban haushi a yayin da West Brom ta bi Southampton har gida ta doke da ci 3-0.

Wasa tsakanin Wigan ta Tottenham an ta shi ne da ci 2-2 sannan Man City ta doke West Ham da ci 2-1

A yau kuma Sunderland za ta fafata da Aston Villa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI