Kotun Duniya-Kosovo

Za a yanke hukunci kan mutanen dake safarar sassan jikin Bil adama

Kotun Manyan laifuka a Kosovo
Kotun Manyan laifuka a Kosovo www.balcanicaucaso.org

Yau ake saran wata kotun kasashen Turai a Kosovo, dake shari’a kan wasu mutane bakwai da ake zargi da safarar sassan jikin Bil Adama za ta yanke hukunci.

Talla

Alkalan kotun sun saurari ba’asi daga shaidu 80, da suka hada da wadanda suka ba da sassan jikin su, da kuma wadanda suka karba, a zaman kotun sama da 100 da aka yi.

Ana dai tuhumar mutanen ne da jigilar kauyawa daga sassan Nahiyar Asiya inda suke basu euro 15,000 dan cire sassan jikin su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.