Kwallon kwando

Dan wasan kwallon kwandon Amurka Jason Collins ya ce yana mu'amullar jinsi daya

Dan wasan kwallon kwandon kasar Amurka a fagen gasar NBA, Jason Collins ya fito fili ya nuna goyon bayansa akan masu auren jinsi daya, inda ya ce shima ya dade yana wannan mu’amulla ta jinsi daya.

Dan wasan kwallon kwando a fagen NBA na Amurka, Jason Collins
Dan wasan kwallon kwando a fagen NBA na Amurka, Jason Collins Sports Illustrated
Talla

Collins, dan shekaru 34, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da wata mujalla da ake kira “Sports Illustrated,” hakan kuma ya sa ya zamanto dan wasa fitacce a kasar ta Amurka daga fagen wasanni da ya fito ya fadi asalinsa.

Tuni Shugaban kasar Barack Obama da shahararren dan wasan na NBA, Kobe Bryant tare da kamfanin saka kayan wasannin na Nike suka fito suka ya mara mai baya.
Shugaban Obama a shekarar da ta gabata ya nuna goyon bayan sa ga auren jinsi daya.

A shekarar 2007, wani dan wasa kwallon kwando a fagen NBA, John Amaechi ya bayyana cewa shi ma yana irin wannan mu’amulla, koda yake tuni ya yi ritaya daga fagen wasan.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI