French League
PSG ta samu koma baya bayan yin kunnen doki da Valencienne da ci 1-1
Wallafawa ranar:
Kungiyar kwallon kafar Valencienne ta rike Paris Saint Germain a gida da ci 1-1 wanda hakan ya kara jinkirta burin PSG na lashe kofin gasar Faransa na Ligue 1.
Talla
Wannan wasa ya sa tazarar makin da PSG ke da shi a teburin gasar ya koma zuwa bakwai a yayin da ya rage mata wasannin uku kamin a kammala gasar.
Sauran sakamakon wasannin gasar na nuna cewa Montpellier ta doke Brest da ci 2-1, sannan Saint Etienne da Bordaux sun tashi babu ci ko daya a yayin da
Lyon ta doke Nancy da ci 3-0 kana Marseille ta doke Bastia da ci 2-1.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu