French League

PSG ta janye bikin lashe kofin gasar Faransa

Magoya bayan PSG na murnar lashe kofin Gasar Faransa
Magoya bayan PSG na murnar lashe kofin Gasar Faransa REUTERS/Benoit Tessier

Kungiyar kwallon kafar Paris Saint Germain dake Paris, ta janye gudanar da bikin nasarar da ta samu na lashe gasar Faransa, wato French Cup, bayan wata arangama da ‘Yan sanda suka yi da wasu magoya bayanta, wanda ya yi sanadiyar jikkatar mutane da dama.

Talla

A yanzu haka dai an dage bikin zuwa wani lokaci nan gaba.

Lashe kofin da PSG ta yi ya biyo bayan nasarar da ta samu akan kungiyar Lyon a rabnar Lahadin da ta gabata da ci 1-0.

Wannan kuma ita ce nasarar farko da PSG ta samu na lashe kofin gasar cikin shekaru 19.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI