Afghanistan-NATO

Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane shida a Afghanistan

Wani hari da aka kai a Afghanistan
Wani hari da aka kai a Afghanistan DR

Wani harin kunar bakin wake, da aka kai da mota a Kabul, dake kasar Afghanistan, kan tawagar sojojin kasashen waje, ya hallaka fararen hula 6, ya kuma raunana wasu 37. 

Talla

Sayed Kabir Amiri, na ma’aikatar lafiyar Kabul, ya ce gaba daya wadanda harin ya ritsa da su, fararen hula ne.

“Wasu daga cikin wadanda suka mutu ba za a iya gane gawarsu ba saboda sun dagargaje.” Inji Amiri.

Haka zalika, Kakakin tawagar sojojin na NATO, Laftanan Quenton Roechricht ya tabbatar da cewa harin an nemi kai shi ne kan motocin tawagar sojojin.

Tuni kungiyar Hezbi -Islama ta dauki alhakin kai harin a yayin da kungiyar ta NATO ta ki cewa komai game da sojojin ta da suka jikkata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI