Ingila

Beckham zai yi ritaya daga fagen kwallon kafa

Tsohon Kyaftin din Ingila, David Beckham
Tsohon Kyaftin din Ingila, David Beckham REUTERS/Karoly Arvai

Tsohon Kyaftin din kasar Ingila, kuma dan wasan Paris Saint Germaine, David Beckham ya ce zai yi ritaya daga fagen wasan kwallon kafa a karshen wannan kakar wasa. Dan shekaru 38, Beckham ya kwashe shekaru 20 yana taka kwallo a matakai daban daban, ya kuma kasance daya daga cikin fitattun ‘yan wasan kwallon kafar Ingila da ya ke da kima a idon mutune ba ma a kasar sa ba har ma da duniya.  

Talla

Bechkam ya bayyana hakan ne kwanaki kadan bayan kungiyrasa ta PSG ta lashe gasar Faransa a kuma kusan dai dai lokacin da Sir Alex Ferguson wanda ya fito da Bechkam a idon duniya a shekarar 1992 shima ya yi ritaya.

“Gaskiyar magana ita ce wannan shawara da na yi mai wuyan gaske ce, domin har yanzu ina ganin cewa zan iya buga wasa a mataki na sama, sai dai a boye ina gayawa kaina cewa ya kamata na fice tun a lokacin da nake ganiyar tashe na.” Inji Beckham.

Ire iren kungiyoyin kwallon kafa da ya taba bugawa wasa akwai Real Madrid, Los Angeles Galaxy da AC Milan da kuma PSG, wanda hakan ya bashi damar lashe kofunan gasar wasannin guda hudu a kasashe daban daban.

Kuma sau 115 yana bugawa kasarsa ta Ingila wasanni, a lokacin yana Manchester United kungiyar ta lashe gasar sau shida, gasar FA Cup sau biyu kana suka kuma lashe gasar zakarun turai na Champions League a shekarar1999 inda United ta doke Bayern Munich ci 2-1 a wasan karshe.

A cikin irin karramawar da ya samu ta hada da kasancewa mai yada manufar gasar wasannin Olympic da aka yi a London a bara inda aka bashi fitilar ta gasar Olympic ya kai filin wasan.

Bechkma yana da mata mai suna Victoria wacce da ‘yar waka ce a cikin kungiyar mawakan nan na Spice Girls suna kuma da yara hudu.

Zai kuma buga wasansa na karshe ne a ranar 26 ga watan Mayu
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI