French League

Takaddama ta barke tsakanin Ancelotti da hukumomin PSG

Mai horar da 'yan wasan PSG, Carlo Ancelotti.
Mai horar da 'yan wasan PSG, Carlo Ancelotti. REUTERS/Benoit Tessier

Takaddama ta barke tsaknain Mai horar da ‘yan wasan Paris Saitn Germaine, Carlos Ancelotti da hukumomin kungiyar. Ancelotti dai ya bayyana cewa zai bar kungiyar ta PSG domin komawa horar da ‘Yan wasan Real Madrid da aka kyankyasa masa, wato inda zai maye gurbin Jose Maurinho, to amma hukumomin kungiyar ta PSG sun ce sam hakan ba za ta yiwu ba domin akwai sauran shekara daya da ya rage mai na kwantirakinsa da kungiyar. 

Talla

Shugaban kuniyar na PSG, Nasser Al- Khelaifi ya ce, ya kamata idan mutum ya saka hanu a kwantiraki to ya yi kokari ya ga cewa ya mutunta wannan kwantiraki.

Ancelotti wanda ya taba horar da ‘Yan wasan Chelsea da AC Milan ya kwashe watanni 18 ne kawai yana horar da ‘yan wasan na PSG.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI