French League

Zan fice daga PSG idan ba a magance matsalolin cikin gida ba- Ibrahimovic

Dan wasan PSG, Zlatan Ibrahimovic.
Dan wasan PSG, Zlatan Ibrahimovic. REUTERS/Benoit Tessier

Dan wasan Paris Saint Germaine, Zlatan Ibrahimovic, ya ce akwai yiwuwar zai fice daga kungiyar ta PSG idan dai har kungiyar ba ta magance matsalolin dake addabata a bayan a cikin gida ba. 

Talla

Ya bayyana cewa, ana shi ra’ayin yana so mai horar dasu, wato Ancelotti ya ci gaba da aikinsa a kungiyar inda ya kara da cewa buga kwallo a kasashen Spain da Italiya ya fi kwanciyar hankali.

Dan shekaru 31, Ibrahimovic wanda a da ya taba bugawa AC Milan, Ajax, Barcelona da kuma Juventus ya zira kwallaye 29 tun zuwan shi kungiyar ta PSG daga kungiyar AC Milan. Shine kuma ya lashe kyautar gwarzon kakar wasa ta bana a fagen gasar ta Faransa, ko kuma French Ligue.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI