Kwallon kafa

Lazio ta lashe kofin gasar Italiya na cikin gida bayan doke AS Roma da ci 1-0

'Yan wasan Lazio na murnar lashe kofin Italiya bayan doke AS Roma da ci 1-0
'Yan wasan Lazio na murnar lashe kofin Italiya bayan doke AS Roma da ci 1-0 www.independent.com.mt

A jiya ne kuma kungiyar Lazio ta kasar Italiya ta lashe kofin gasar Italiya, wato Italian Cup bayan ta doke Roma da ci 1-0.

Talla

Har ila yau Lazio a yanzu haka ta samu damar shiga gasar Europa League na kakar wasa mai zuwa. Dukkanin kungiyoyin biyu basu samu damar taka rawar gani ba a fagen gasar Serie "A".

Dan wasan Lazio Senad Lucil ne dai ya zira wa Lazio kwallonta a miniti na 20. An dai buga wasan cikin tsauraran matakai inda aka aike da 'Yan sanda sama da 2,000 a karawar karshe wacce ita ce ta farko da kungiyoyin biyu suka taba haduwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI