Faransa

Faransa ta haramtawa shugaban Madagascar shiga kasarta

Ministabn harkokin wajen kasar Faransa, Laurent Fabius
Ministabn harkokin wajen kasar Faransa, Laurent Fabius Reuters

Faransa ta haramta wa shugaban kasar Madagascar, Andry Rajeolina da kuma mai dakinsa shiga kasar a daidai lokacin da kasashen duniya ke ci gaba da yi wa shugaban matsin lamba domin janyewa daga takarar neman mukamin shugabancin kasar da za a gudanar a nan gaba.

Talla

Tun da jimawa ne dai Faransa ta bayyana rashin amincewarta da tsayawar Rajeolina da kuma wasu mutane biyu takarar neman mukamin shugabancin kasar. Wadanda ake neman su janye daga takarar.

A ranar Laraba mai zuwa ne dai kungiyar ci gaban tattalin arzikin kasashen yankin kudancin Afirka SADC za ta gudanar da taro na musamman domin sanar da daukar matakai a kan wasu daga cikin ‘yan takarar da suka hada har da shugaba Andry Rajeolina.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.