Dan takarar Jam’iyyar RPM ke kan gaba a Zaben Mali
Wallafawa ranar:
Ministan da ke kula da harakokin cikin gidan kasar Mali Colonel Moussa Sanki Koulibaly ya bayyana cewa an samu kashi daya bisa uku na zaben shugabancin kasar kuma dan takarar Jam'iyar RPM Ibrahim Bubakar Kaita ne ke kan gaba nesa ba kusa ba, sai dai kuma ya ce sun dauki dukkanin matakan da suka dace idan ta kama a je zagaye na biyu. Daga Bamako wakilinmu na musaman Mahaman Salisu Hamisu ya aiko mana da rahoto.