An girke dakaru a Tripoli na Libya
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sauti 02:58
Hukumomi a kasar Libya sun aike da sojoji akan manyan titunan birnin Tripoli, bayan da aka share tsawon kwanaki uku ana ba ta-kashi tsakanin bangarorin mayaka masu hamayya da juna a birnin. Akalla mutane fiye da 40 suka mutu. Abdoulaye Issa ya tattaunawa da wani mazauni birnin na Tripoli da ya bukaci a sakaye sunansa saboda dalilai na tsaro, ya kuma yi ma sa Karin bayani kan halin da ake ciki.