Faransa-Chadi

Faransa tana fatar dakarun Chadi kada su fice Afrika ta tsakiya

Ministan harakokin wajen Faransa Laurent Fabius
Ministan harakokin wajen Faransa Laurent Fabius REUTERS/Enrique De La Osa

Ministan harakokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius ya bayyana fatan ganin dakarun kasar Chadi sun ci gaba da aiki a rundunar samar da zaman lafiya a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ba tare da sun fice ba kamar yadda suke nufi.

Talla

Fabius ya bayyana cewa, yana fatan wannan mataki da Chadin ta dauka na janye dakarunta daga cikin rundunar samar da zaman lafiya a kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya ba matakin karshe ba ne.

Ministan ya kara da cewa, dakarun kasar Chadi mayaka ne na kwarai, da ke makwabtaka da Afrika ta tsakiya da ke fama da rikici, don haka a cewar Fabius ya zama wajibi a tabbatar da tsaro.

Fabius ya bayyana cewa, shugaba Deby ya shaida masa cewa, ya bayar da gudumuwar dakaru wajen gudanar da ayyukan jinkai, tare da rasa rauyukansu, ba tare da ya bukaci samun wata riba ba.

A farkon wannan wata na Afrilu ne, gwamnatin Cchadi ta bayyana janye dakarunta 850 da ke aikin samar da zaman lafiya sakamakon abinda ta kira bata sunan da ake yi wa dakarunta a kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.