Ilimi Hasken Rayuwa

Google zai fara share bayanan sirri a Turai

Sauti 10:00
Tambarin Kamfanin google Injinin Bincike a Intanet
Tambarin Kamfanin google Injinin Bincike a Intanet @Google

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa ya tattauna ne game da Kamfanin Google wanda mahukuntan Turai suka bukaci ya dauki matakan share bayanan mutane na sirri da suke bukata karkashin dokar sirinta rayuwarsu. Shin ya girman al’amarin ya ke, sannan ya hakan zai shafi ‘Yanci na samun bayanai musamman ga aikin bincike na Jarida?

Talla

Yanzu haka Kamfanin Injinin bincike na Google yace ya karbi bukatun dubban mutanen Turai wadanda ke neman a share bayanansu na sirri da suke bukata a Intanet bayan Kotun Turai ta bukaci kamfanin na bincike ya aiwatar da bukatar karkashin dokar kare sirrin rayuwar mutane.

Bayan da kotun Turai ta yanke hukuncin, google ya bude shafi domin ba masu bukatar a share bayanansu damar aikawa da bukatarsu tare da cika wasu sharudda da kamfanin ya shata.

Google yace yana samun bukatar daga mutanen na Turai a cikin dakoki bakwai, musamman daga ‘yan siyasa da wadanda ke son a dakile hoto ko bidiyonsu na tsaraici.

Shirin ya tattauna da Farfesa Abdalla Uba Adamu Malami a Jami’ar Bayero a Kano Najeriya, da Dr Jameel Yusha’u Mai sharhi kan lamurran yau da kullum da kuma Dr Umar Saleh Gwami Tsohon Malamin Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Ko ya suke kallon girman wannan mataki lura da girman google a fannin bincike a Intanet? Sannan ya hakan zai yi tasiri ga ‘yancin samun bayanai musamman ga aikin Jarida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.