Kwallon kafa

Ban ajiye aiki na da Super Eagles ba - Keshi

Mai horar da 'yan wasan Najeriya, Stephen Keshi
Mai horar da 'yan wasan Najeriya, Stephen Keshi

Mai horar da ‘yan wasan Super Eagles na Najeriya, Stephen Keshi ya musanta rahotanni da suke nuna cewa ya ajiye aikin na horar da ‘yan wasan kasar, inda ya ce kadu matuka da ya ji ana yayata labarin.

Talla

Keshi ya ce ya san dai ya gayawa ‘yan wasansa cewa watakila wannan shine wasansa na karshe a matsayin sa na mai horar da su.

Ya kuma da cewa ya gayawa ‘yan wasan cewa kwantirakinshi zai kawo karshe ne a karshen wannan gasa, kuma ba a yi mai tayin wani sabon kwantiraki ba.

A cewar Keshi ba a ajiye aiki a shafukan jaridu kamar yadda rahotanni suka nuna ba.

“Na kadu matuka da na ga kafofin yada labarai na duniya suna cewa na ajiye aiki na.” Inji Keshi a wata sanarwa da ya fitar ta hanun jami’in kula harkoki da ‘yan jarida, Ben Alaiya.

Ko da Keshin ya bayyana cewa akwai kasashe da dama dake nuna sha’awar su dauke shi a aiki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.