EU-Birtaniya

Birtaniya ta soma kai hare haren sama a Syria

Firaministan Birtaniya David Cameron
Firaministan Birtaniya David Cameron REUTERS/Suzanne Plunkett

Majalisar Birtaniya ta amince da shirin gwamnatin kasar na shiga cikin jerin kasashen dake kai hare haren sama cikin kasar Syria da zummar murkushe kungiyar mayakan ISIS.

Talla

Yan Majalisu 397 suka amince da bukatar Firaminsita David Cameron yayin da 223 suka hau kujerar naki.

Sakataren Tsaron kasar Philip Hammond yace daren yau ake saran jiragen su fara kai harin, yayin da Firaminista Cameron ya yaba da matakin da Majalisar ta dauka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.