Harin kunar bakin wake a Damascus
Wasu tagwayen hare-hare sun halaka sama da mutane 60 a birnin Damascus na kasar Syria.Damascus wurin da ake kalo a matsayin cibiyar Gwamnatin kasar ta Syria ,birnin ya jima ya na fama da hare-haren yan ta’ada kama daga shekara ta 2011,duk da yake dakarun kasar sun tabbatar da kare wannan gari.
Wallafawa ranar:
A wanan harin kunar bakin wake an dai tabbatar da cewa daya daga cikin yan ta’adan dake dauke da jigidar bama-bamai ya tarwartsa kansa a kudu maso gabacin birnin .
Hari mafi muni shine na shekara ta 2016 wanda mutane 134 suka mutu,wasu 97 suka samu mugun rauni, harin da kungiyar Isil ta dau alhakin sa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu