Faransa

Sarkozy zai daukaka kara

Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy a a lokacin da yake kare kansa atashar TF1.
Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy a a lokacin da yake kare kansa atashar TF1. Handout / TF1 / AFP

Nicolas Sarkozy da ya jagoranci kawancen kasashen da suka yaki mulkin Kaddafi wanda ya yin alkawarin zubar da jinni a Benghazi, ya musanta zargin da ake masa na karbar kudade daga hannun Libya a yakin zaben san a shekara ta 2007. 

Talla

Sarkozy na magana ne a gidan talabijen na TF1 na kasar ta Faransa.

Nicolas Sarkozy a tashar TF1 na Faransa

Daya daga cikin na hannun damar tsohon Shugaban Libya Moftah Missouri ya gaskanta goyan bayan marigayi Kadhafi na  kudi milyan 20 na dala zuwa dan takara Nicolasa Sarkozy a shekara ta 2007.

Moftah Missouri daya daga cikin na hannun damar Kadhafi

Moftah ya bayyana cewa Sarkozy da Kadhafi sun yi haduwar farko ne a shekara ta 2005.

Lauyan tsohon Shugaban kasar Thierry Herzog ya sanar da aniyar su na daukaka kara.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.