Faransa

Belgium ta mikawa Faransa wanda ake tuhuma a harin Paris

Sojin Faransa na kula da sha'anin tsaro a kasar
Sojin Faransa na kula da sha'anin tsaro a kasar Reuters

Belgium ta mika wa ma’aikatar shara’ar Faransa wani da ake tuhuma da hannu a harin da ‘yan ta’adda suka kai tare da kashe mutane 130 a birnin Paris 2015.

Talla

Osama Krayem an cafke shi ne tun cikin shekara ta 2016 a Belgium, bayan wani harin ta’addanci da aka kai birnin Bruxelles, yayin da masu gabatar da kara a Faransa ke cewa suna tuhumar sa da hannu a harin na birnin Paris da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 130.

Gwamnatin Faransa ta jadada aniyar ta na yakar ta'adanci tareda daukar matakan zurfafa bincike zuwa wasu daga cikin mutanen da ake sa ran suna  da hannu a batutunwan da suka shafi ta'adanci a kasar ta Faransa.

Yanzu haka akwai wasu yan kasashen waje da ake ci gaba da tsare da su bisa laifin ta'adanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.