Diflomasiya

Baraka na dada bayyana tsakanin Amurka da Turai

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani da Donald Trump Shugaban Amurka
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani da Donald Trump Shugaban Amurka scroll.in

Takaddama tsakanin Amurka da kasashen Turai kan Iran ta sake fitowa fili a taron Majalisar Dinkin Duniya dake gudana yanzu haka, bayan da kungiyar ta bayyana shirin gudanar da cinikayya da Iran ba tare da barin takunkumin Amurka yayi tasiri kan kasar ba.

Talla

A wani yanayi da ake danganta shi da lokacin da aka shirya mamaye kasar Iraqi a shekarar 2003, Amurka ta zargi kawayen nata da cin amana, yayin dasu kuma suka bayyana mata karara cewar ba zasu bada kai bori ya hau ba.

Bayan wani taro da suka gudanar, Babbar jami’ar diflomasiyar Turai Federico Mogherini tare da ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif sun shaidawa duniya matakan da suka dauka na kaucewa takunkumin Amurkar, yayin da Sakataren harkokin waje Mike Pompeo da ya kwashe watanni yana kira ga kasashen duniya su daina sayen man Iran daga watan Nuwamba mai zuwa, ya bayyana takaicin sa da matakin.

Mai baiwa shugaba Trump shawar kan harkokin tsaro, John Bolton ya bayyana Turai a matsayin masu karfin farfaganda da kuma gazawa wajen cika alkawari, inda yake cewa ba zasu bari wata kasa koda na Turai ne ta kaucewa takunkumin na Amurka ba.

Shima shugaba Donald Trump a jawabin da ya gabatar ya cacaki shugabannin Iran wadanda ya bayyana su a matsayin masu karkata dukiyar kasar su domin amfanin kan su da kuma haifar da tashin hankali a kasashen dake iyaka da kasar, yayin da shugaba Hassan Rouhani a nashi jawabin ya zargi Amurka a matsayin wadda ke yunkurin kisa juyin mulki a kasar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.