Faransa

Faransa zata binciko yadda ake haifar yara da nakasa a kasar

Wasu yara a gadon asibiti na kasar Faransa
Wasu yara a gadon asibiti na kasar Faransa AFP/Loïc Venance

Faransa ta kaddamar da wani sabon bincike a sassan kasar game da yadda ake haifar yara da nakasa a hannayensu wanda ke matsayin barazana ga lafiya. Binciken na nuna ana haifar akalla yara 150 kowacce shekara da makamanciyar nakasar.

Talla

Matakin gwamnatin na zuwa ne bayan watsi da sakamakon binciken da ma’aikatar lafiyar kasar ta gudanar tun da farko da ke nuna cewa babu wani dalili da ke haddasa haifar yaran da nakasa.

Francoise Bourdilon shugaban sashen kula da lafiyar al’umma na kasar ta Faransa, ta ce nan da watanni 3 za a tabbatar da hakikanin abin da ke haddasa haifar yaran da nakasa.

Bayanan farko dai na nuna cewa matsalar ta fara tsananta ne daga shekarar 2007 inda aka haifi yara 14 da nakasa a hannu, sai dai yanzu haka wani sabon bincike ya ce tun a shekarar 2000 an samu makamanciyar matsalar kan yara akalla 11 a yankin Ain gab da kan iyakar kasar da Swiziland amma aka gaza sanar da mahukunta.

Dama dai an gudanar da binciken na farko ne a jihohin Faransa 3 da suka kumshi kudancin Britaniya da aka haifi yara 3 masu matsalar a 2007 sai Loire-Atlantique mai yara 4 a shekarar 2011 sai kuma jihar Ain da aka haifi yara 7 masu nakasa a hannu.

A cewar Francoise Bourdilon kusan yara 150 ake haifa a Faransa da nakasa a hannayensu matakin da ta ce suna kan binciken gano ko yana da alaka da abincin da iyayen ke ci ko kuma nau’in maganin da su ke amfani da shi.

Ko a shekarar 1950 duniya ta fuskanci matsalar haifar yara da nakasa a kafa da hannu wanda daga bisani bincike ya nuna cewa na da nasaba da wani magani da mata masu juna biyu ke amfani da shin mai suna Thalidomide wanda hukumomi suka haramta amfani da shi a shekarar 1960.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.