Turkiya-Saudiya

An hallaka Jamal Khashoggi ta hanyar daddatsa shi

Mai shigar da kara na kasar Saudiya Saoud ben Abdallah al-Muajab a Turkiya
Mai shigar da kara na kasar Saudiya Saoud ben Abdallah al-Muajab a Turkiya REUTERS/Kemal Aslan

Turkiya ta fitar da wasu sabbin bayanai da ke nuna cewa an hallaka fitaccen dan jaridar Saudiyan nan Jamal Khashoggi jim kadan bayan shigarsa ofishin jakadancin Saudin da ke Istanbul ranar 2 ga watan Oktoba ta hanyar daddatsa shi tare da yi wa gangar jikinsa filla-filla.

Talla

Babban mai shigar da kara na Turkiya, Irfan Fidan a bayanai karon farko da ya ke fitarwa game da kisan Jamal Khashoggi ya sanar da cewa an hallaka fitaccen dan jaridar ne jimawa kadan bayan shigarsa Ofishin jakadancin da ke birnin Santanbul a Turkiya.

Kalaman na Irfan na zuwa ne sa’o’I kalilan bayan ganawarsa da takwaransa na Saudiya Sheikh Saud al-Muajab wanda ya isa kasar ranar lahadin makon jiya dangane da batun kisan na Khashoggi wanda ya yi kaurin suna wajen caccakar gidan sarautar kasar.

A kalaman na Irfan bayan ganawar ta su wadda ta ginu kan sanar da gaskiyar yadda Khashoggi ya rasa ransa a Ofishin jakadancin na Saudiya, ya ce tun farko jami’an sun shake wuyan dan jaridar tare da hana masa lumfashi wanda ya yi sanadin mutuwarsa, kafin daga bisani su daddatsa shi,su kuma sanya shi a akwati tare da ficewace da shi daga Ofishin don watsar da gangar jikinsa.

dai bayanan baya-bayan nan da Turkiyan ke fitarwa ta ce babu yadda za a yi a iya kashe Khashoggi ba tare da sanin shugabancin gidan sarautar Saudiyan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.