Faransa

Faransa ta karawa kamfanonin Amurka haraji

Zanga-zangar Faransa
Zanga-zangar Faransa

Gwamnatin Faransa tace zata gabatar da wani sabon haraji kan manyan kamfanonin sadarwa daga ranar 1 ga watan Janairu mai zuwa domin cike gibin sassaucin da aka yiwa talakawa.Ministan kudi Bruno Le Maire yace Faransa na zakewa wajen ganin manyan kamfanoni irin su Apple da Facebook da Amazon da Google sun biya karin haraji ne daidai da yadda suke gudanar da harkokin kasuwancin su a duniya.

Talla

Ministan yace ana saran kamfanonin su biya euro miliyan 500 a matsayin harajin daga farkon shekara mai kamawa.

Kin biyan haraji mai tsoka daga kamfanonin na Amurka ya dade ya na haifar da takun saka tsakanin nahiyoyin biyu.

Ofishin ministan cikin gidan Faransa ya bayyana cewa adadin mutanen da suka gudanar da zanga-zanga ya ragu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI