A shirin namu na yau zai karkata ne zuwa kasar Kamaru, inda zai duba tarihin kabilar hausawa daya daga cikin kabilu Kamaru sama da 200 da Allah ya zuba a kasar, kabilar da ake samu a kasashe da dama na Afrika da suka hada da Najeriya,Nijar, Ghana, Tchad, Sudan, Jamhuriya Afrika ta tsakiya .Shirin al’adun mu na gado shirin da kan tattauna lamarun da suka shafi al’adu a Duniya tare da Mahaman Salisu Hamisu.