Rasha

Netherlands na shirin gurfanar da Rasha a gaban kotu

Makami da aka yi amafani da shi wajen harbo jirgin saman Malaysia
Makami da aka yi amafani da shi wajen harbo jirgin saman Malaysia REUTERS/Francois Lenoir

Gwamantin kasar Netherlands na shirin gurfanar da Rasha a gaban kotu bisa zargin cewa kasar ta taka rawa wajen haddasa hadarin jirgin saman kamfanin Malaysia Airlines lokacin da yake ratsa sararin samaniyar Ukirain wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 283.

Talla

Masu binciken hadarin jirgin MH17 mallakar Malaysia da ya fadi a gabashin Ukraine a shekarar 2014 dauke da fasinjoji 298 sun bayyana cewar makamin rundunar sojin Rasha ne ya kakkabo jirgin.

Shugaban kwamitin da ya gudanar da binciken, Wilbert Paulissen, dan kasar Netherlands ya ce, gaba dayansu sun yi itfifakin cewar makamin BUK-TELAR da aka yi amfani da shi wajen kakkabo jirgin ya fito ne daga runduna ta 53 ta sojojin Rasha da ke da sansani a Kursk.

Paulissen ya shaida wa manema labarai cewar, rundunar ta 53 na daga cikin rundunonin sojin Rasha, kuma makamin da suka yi amfani da shi na da fuskoki da dama.

An dai harbo jirgin MH17 mallakar kasar Malaysia ne ranar 17 ga watan Yulin shekarar 2014, lokacin da yake kokarin ratsa sararin samaniyar Ukraine, bayan ya tashi daga Amsterdam zuwa Kuala Lumpur dauke da fasinjoji 298 tare da matuka jirgin, akasarinsu 'yan kasar Netherlands.

Kasar Rasha ta dade tana musanta zargin da ake ma ta na kakkabo jirgin.Lamarin dai ya faru ne a shekara ta 2014, kuma fasinjoji 196 daga cikinsu ‘yan kasar ta Netherlands ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI