Korea ta Arewa-Amurka

Yiwuwar sake ganawa tsakanin Trump da Kim Jong-Un

Shugaba Donald Trump da Kim Jong Un na koriya ta Arewa
Shugaba Donald Trump da Kim Jong Un na koriya ta Arewa 路透社。

Shugaban Amurka Donald Trump na fatan sake yin ganawa ta biyu da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong UN a farkon shekara mai zuwa kamar dai yadda sakataren wajen Amurka Mike Pompeo ya sanar.

Talla

Pompeo ya ce akwai kwarin gwiwa dangane da yiyuwar samun wannan ganawa tare da yin tattaunawa dangane da batun nukiliyar kasar, bayan ganawar da mutanen biyu suka a cikin wannan shekara.

A kokarin kawo karshen tankiyar dake tsakanin kasashen biyu sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya sanar da sunan Stephen Biegun a matsayin jakada na musamman mai shiga tsakani a tattaunawar Korea ta Arewa da Amurka. Mr Stephen wanda shi ne tsohon mataimakin shugaban kamfanin motoci na Ford, ya ziyarci Korea ta Arewan bisa rakiyar Mr Pompeo.

Stephen na a matsayin mai shiga tsakani kan tattaunawar ta Amurka da Korea da nufin cewa zai rika sanar da Washington halin da ake ciki kan shirin kwance makaman nukiliyar na Korea ta Arewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI