Turai

Ana zargin Ronaldo da fyade a Las Vegas na Amurka

Cristiano Ronaldo dan wasan Fotugal
Cristiano Ronaldo dan wasan Fotugal REUTERS/Massimo Pinca

Yan Sanda birnin Las Vegas na kasar Amurka na daf da bayar da samacin a kamo musu dan wasan kasar Fotugal Cristiano Ronaldo.Ana zargin wannan dan wasa da aikata fyade sama Kathryn Mayorga wata yar kasar Amurka a shekara ta 2009.

Talla

Yan Sandan Las Vegas sun bukaci wannan dan wasa da ya bayar da hadin kai domin a gudanar da bincike daga kwayoyin halitar jikin dan Adam da aka sani da AND na sa, da za danganta da wanda ke saman rigar wannan mata a lokacin da suke tare a cewar masu bincike.

Dan wasan Cristiano Ronaldo ya musanta wannan zargi tareda bayyana cewa ,ya na daga cikin masu adawa da irin wadanan miyagun dabi’u da suka hada da fyade, ya kuma bayyana cewa ana kokarin shafa masa kajin kaji ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI