Birtaniya na garkuwa da kungiyar Turai
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana kin amincewa da ci gaba da garkuwa da Kungiyar tarayyar turai ta EU, kan rashin samar da mafita ga batun ficewar Britaniya daga kungiyar sakamakon ci gaba da fatali da duk wata mafita da aka gabatar da majalisar dokokin kasar ta Britaniya ke yi .
Yayinda ya rage kwanaki 10 wa’adin da aka dibarwa Birtaniya ya cika,yan Majalisu sun kasa baiwa Firaministar kasar Theresa May hadin kai.
Kar da a manta cewa Firaministar Birtaniya Theresa May da ta fuskanci bore daga 'ya'an Jam’iyyar ta konzabatib ta ce ba za ta jagoranci Jam’iyyar zuwa zaben shekarar 2022 ba, domin za ta sauka daga mukamin ta bayan kammala shirin ficewar kasar daga kungiyar kasashen Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu