Asiya

Bayan kwashe shekaru 27 a sume,wata mata ta dawo cikin hayyacin ta

Wani asibiti da ake kwantar da marasa lafiya
Wani asibiti da ake kwantar da marasa lafiya pixabay

Wata mata da ta kwashe shekaru 27 a sume a sakamakon buguwar kwakwalwar da tayi saboda hadarin mota a Daular Larabawa, a karon farko ta bude idanun ta kana ta dawo cikin hayyacin ta kamar yadda iyalan ta suka bayyana.

Talla

Matar mai suna Munira Omar mai shekaru 32 lokacin da ta gamu da hadarin a shekara 1991, lokacin da ta dauko dan ta daga makaranta, ta farfado ne bayan tayi dogon jinya a wani asibitin Jamus inda aka kula da ita.

Dan ta Omar wanda suka yi hadari tare, mai shekaru 32 yanzu haka, ya bayyana cewar shi dama yayi imanin mahaifiyar sa zata warke.

Omar yace likitoci da dama sun shaida musu cewar kar su sanya wata fata na tashin mahaifiyar ta sa bayan shekaru 15 zuwa 20 da hadarin, amma yaki amincewa da haka.

Iyalan Munira sun ce tun a watan Mayun bara ta farfado, amma suka ki shaidawa mutane saboda kar a dame ta.

Omar yace yanzu haka mahaifiyar ta sa mai shekaru 60 na cikin yanayi mai kyau a gidan su dake Daular Larabawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.