Amurka- Iran

Za mu yi raddi mai zafi kan Iran muddin ta kai mana hari - Trump

John Bolton mai taimakawa shugaban Amurka ta bangaren tsaro
John Bolton mai taimakawa shugaban Amurka ta bangaren tsaro Reuters

Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi Iran da cewa za ta dandana kudarta muddin ta kuskura ta kaiwa Amurka ko kuma muradunta hari, domin za ta maida raddin da ka iya ruguza kasar ta Iran.

Talla

A Gargadin na Trump da ya wallafa a Shafinsa na Twitter y ace shugabannin Iran basa fahimtar komai idan ba an nuna musu karfi da iko ba.

Wannan na zuwa bayan da Sakataren Tsaro na Amurka John Bolton ya gargadi Iran da kada ta sukurkuta taron sulhu game da Gabas ta Tsakiya da aka fara yau a Bahrain.

Yayin wata ziyara John Bolton ya bayyana cewa, Iran na ta wasu take-taken ta, tareda yiwa Amurka tsiwa, domin hatta taron da ake yi a Bahrein karkashin jagorancin Amurka, Iran na iya yin katsalandan a ciki.

A makon jiya ne dai Iran ta kakkabo wani jirgin sama na Amurka maras matuki a ciki, daya ratsa sararin samaniyarta, zargin da Amurka ta musanta.

Amurka a nata bangaren ta zargi Iran da laifin kai hare-haren ta’addanci kan jiragen ruwa dake dakon albarkatun mai a yankin Gulf, zargin da Iran itama ta musanta.

A yau litinin ne dai ake fara wannan taro a Manama dake Bahrein wanda Amurka ta shirya da niyyar gabatar da wasu tsare-tsaren bunkasa tattalin arzikin yankin duk dai don ganin an samu zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falesdinawa.

Karkashin tsarin za’a zuba kudaden da suka kai bilyan 50 na dalla cikin shekaru 10 a yankin Falesdinawa da kasashen larabawa dake kusa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.