Wasanni

Kungiyoyin Afrika ba su gamsu da na'urar VAR a gasar cin kofin Duniya na mata

Wallafawa ranar:

Kasashe da dama ne suka yi tir da Allah wadai zuwa hukumar Fifa dangane da wannan na’urar bidiyo ta VAR da aaka yi amfani da ita a lokacin gasar cin kofin Duniya ta mata dake ci gaba da gudanaa Faransa.Tsokaci dake zuwa biyo bayan kawar da kungiyoyin mata na kasashen Afrika.Cikin shirin Duniyar wasanni,zaku ji ko a in aka kwana dangane da gasar cin kofin Nahiyar Afrika a Masar.

Na'urar VAR da ake amfani da ita a filin wasa na kwallon kafa
Na'urar VAR da ake amfani da ita a filin wasa na kwallon kafa The Times
Talla

Idan aka yi tuni hukumar kula da kwallon kafa ta Afrika CAF, ta amince da shirin soma amfani da fasahar taimakawa alkalin wasa da maimaicin bidiyo VAR, a gasar cin kofin nahiyar ta Afrika AFCON na Masar a wannan shekara.

CAF ta yanke shawarar ce a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, a lokacin gasar cin kofin nahiyar Afrika ajin matasa ‘yan kasa da shekaru 20.

Fasahar VAR ta karbu ne bayan soma amfani da ita a gasar cin kofin duniya ta 2018 da Rasha ta karbi bakunci, hakan yasa a halin yanzu hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA ta kaddamar da amfani da fasahar a kakar wasa ta bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI