Duniya

Amurka ba zata ja da baya gaban China

Donald Trump Shugaban Amurka ya na mai gargadi ga hukumomin China
Donald Trump Shugaban Amurka ya na mai gargadi ga hukumomin China REUTERS/Yuri Gripas

Akwai alamun dake nuna cewa tsugune bata kare ba a rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da China bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya aikewa China da sakon kada ta dauka zai sasanta da ita game da batun cinikayya tsakanin su.

Talla

Bayan samun cacar baka na kusan wata daya a rikicin da aka fara tsakanin kasashen biyu, China da Amurka, Shugaba Trump ya fadi cikin sakon tweeter cewa yana ganin Sinawa dake tattaunawa da Amurka na farin ciki, cewa za’a yi waje road dashi ne a zaben badi.

Wadan nan kalaman na Trump bisa dukkan alamu na kara dama lissafi, a dangantan kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

A cewar Donald Trump yana sane cewa China na kaunar zumunci da duk wata sabuwar Gwamnati a Amurka, amma kuma dai da sauran lokaci na tsawon watanni 16 idan ma har ma wa’addin wannan mulki da yake yi shine na karshe.

Yace idan kuma har ya tsallake to kuwa kasar China zata dandana kudarta.

Kafofin sadarwa dake Beijing sun sanar da cewa wakilan majalisar Dattijai na Amurka , daga jamiyar Republican Steve Daines da David Perdue sun gana da mataimakin firiamiyan China Liu He a birnin Beijing don tattauna batun kasuwancin na kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.