Wasanni

Mourinho ya maye gurbin Pochentino

José Mourinho sabon mai horar da kungiyar Tottenham
José Mourinho sabon mai horar da kungiyar Tottenham Reuters/Carl Recine/File Photo

Dan kasar Fotugal Jose Mourinho ya maye gurbin dan kasar Argentina Maurico Pochentino da kungiyar kwallon kafar Tottenham ta yi waje da shi.A sanarwar da kulob din na Tottenham ya fitar,cimma wannan yarjejeniya da Mourinho na da nasaba da irin rawar da ya taka a baya kasancewa ya taba horar da kungiyoyi da suka hada da Chelsea da Manchesterd United a gasar Premier ta Ingila kamar dai yada kamfanin dilanci labaren Faransa na AFP ya ruwaito.

Talla

Sanarwar da kungiyar ta gabatar yace Mourinho wanda tsohon mai horar da kungiyoyin Chelsea da Manchester United ne, ya sanya hannu kan kwangilar da zata kais hi zuwa karshen kakar shekarar 2022 zuwa 2023.

Shi dai Pochettino mai shekaru 47 ya fara aiki ne da Tottenham Hotspur a shekarar 2014 bayan ya bar kungiyar Southampton, inda ya sauya alkiblar kungiyar ta zama daya daga cikin wadanda ake tinkaho da su a Ingila da kuma gasar cin kofin zakarun Turai, inda suka kai matakin karshe a karon farko.

Matsalolin da kungiyar ta samu a kakar bana wanda ya bar ta a matsayi na 14 a teburin Premier da kuma samun maki 3 kacal daga wasanni 12 da ta buga, ya harzuka shugabannin kungiyar da magoya bayan ta.

Tuni dai aka fitar da kungiyar Tottenham daga League Cup yayin da Bayern Munnich ta yiwa kungiyar cin kaca 7-2 a gasar cin kofin Turai.

Tuni Mourinho ya bayyana farin cikin sa da nadin da aka masa, inda ya bayyana gamsuwa da zaratan Yan was an dake kungiyar da kuma bangaren yaran da ake horar wa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.