Faransa za ta karrama sojojin ta da suka mutu a Mali
Wallafawa ranar:
A birnin Paris, yau litinin za a gudanar da addu’o’in karrama sojojin Faransa 13 da suka mutu a hatsarin jirgin sama cikin makon da ya gabata a arewacin kasar Mali.Ma’aikatar tsaron Faransa ta fitar da sanarwar da ke nisanta hadarin jiragen yakinta biyu a Mali da ya hallaka sojin kasar 13 da farmakin mayakan jihadi.
Za a dai gudanar da addu’o’in ne karkashin jagorancin shugaba Emmanuel Macron da kuma takwaransa na Mali Ibrahim Boubacar Keita. To sai dai shugaban na Mali na shan kakkausar suka a cikin gida, lura da cewa a cikin makonnin biyu da suka gabata an kashe sojojin kasar sama da 100 amma ba tare da an shirya masu wata jana’iza irin ta karramawa ba.
Fadar Shugaban kasar Mali na kokarin kare manufofin gwamnatin kasar duk da suka da take sha daga kungiyoyi da yan siyasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu