Faransa

Macron zai ci gaba da goyan bayan dakarun Faransa

Addu'o'in musamman don karrama sojojin Faransa da suka mutu a Mali
Addu'o'in musamman don karrama sojojin Faransa da suka mutu a Mali REUTERS/Charles Platiau

Daruruwan mutane ne suka yi gangami a birnin Paris domin karrama sojojin kasar 13 da suka mutu sakamakon hadarin jiragen sama a Mali, lokacin da suke yaki da yan ta’adda.Shugaba Emmanuel Macron da takwaran sa na Mali, Ibrahim Boubacar Keita suka jagoranci bikin.

Talla

Shugaban Faransa ya bayyana alhinin sa tareda daukar alkawali na dafawa dakarun kasar a yakin da suke yi da yan ta'adda a Mali.

Faransa na daya daga cikin manyan kasashe dake taka gaggarumar rawa a yakin da take yi da yan ta'adda a yankin Sahel.

Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita da ya halarci wadanan addu'o'i ya jajintawa iyalan sojojin da suka rasa rayukan su a fagen yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.