Duniya

Taron cika shekaru 70 da kafuwar kungiyar Nato/ Otan

Yau Shugabannin kasashen dake cikin kungiyar kawancen tsaro ta NATO ke taron cika shekaru 70 da kafuwar kungiyar su a London, amma rashin jituwa da sukar juna kan batutuwan da suka shafi kudade da kasuwancin na yiwa taron barazana.

Cibiyar kungiyar Nato/ Otan
Cibiyar kungiyar Nato/ Otan REUTERS/Ints Kalnins
Talla

Shugabannin kasashen kungiyar 29 sun isa London ne domin fafatawa kan irin gudumawar da kowacce kasa ke bayarwa da kuma yadda zasu fuskanci barazanar Rasha wanda shine babban kalubalen dake gaban su da zai dada jaddada muhimmancin kungiyar.

Shugaba Donald Trump na Amurka ya isa London da zummar ganin kasashen Turai sun kara yawan kudaden da suke zubawa a aljihun kungiyar, maimakon barin Amurka tana daukar nauyi su kuma suna mayar da hankali wajen kare kan su.

Shugabannin kungiyar na fatar ganin sanarwa Sakatare Jens Stoltenberg na bukatar kara kudaden da kasashe ke zubawa, na iya kwantar da hankalin shugaba Trump, wanda ya cacake su wajen taron shekarar 2018.

Stoltenberg yace daga nan zuwa shekara mai zuwa, kasashen da basa kawance da Amurka zasu kara kudaden da suke kashewwa ta fuskar tsaro zuwa Dala biliyan 130.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI