Turai

Borris Johnson na daf da lashe zaben Birtaniya

Borris Johnson Firaministan Birtaniya yan lokuta da fitar da sakamakon farko na zaben  kasar
Borris Johnson Firaministan Birtaniya yan lokuta da fitar da sakamakon farko na zaben kasar REUTERS/Peter Nicholls

Masu neman ganin Birtaniya ta ci gaba da kasancewa a kungiyar Tarayyar Turai suna daf yin rashin nasara a fafutukar su, bayan alamu na nuni da cewa jam’iyyar Conservative mai mulki za ta yi nasara a babban zaben kasar .A daya wajen shugaban jam’iyyar adawa ta Labour Jeremy Corbyn ya bayyana cewa ba zai jagoranci jam’iyyar a zabuka masu zuwa ba.

Talla

Kuri’ar jin ra’ayi da aka kada a daren jiya Alhamis, na nuni da cewa jam’iyyar Conservative ta Boris Johnson ta samu gagarumin rinjaye, abin da zai ba shi damar aiwatar da batun ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai.

Sakamakon kuria’ar ficewar ya yi hasashen cewa jam’iyyar Conservatives za ta lashe kujeru 368 cikin 650 na majalisar dokokin Birtaniya, yayin da babban jam’iyyar adawa ta Labour ta tsira da kujeru 191, sai kuma jam’iyyar Scottish National Party ta tashi da kujeru 55.

Jam’iyyar Liberal DEMOCRATS karkashin jagorancin Jo Swinson kuwa za ta tashi da kujeru 13, kamar yadda sakamakon kuri’ar ya bayyana.

Masana na cewa, babban jam’iyyar adawa ta Labour ta sha wannan kayen ne sakamakon rashin bijirowa da zabi mai inganci kan batun yarjejeniyar jam’iyyar barin Turai.

A safiyar yau Juma’ar nan ake sa ran samun sakamakon karshe, kuma tabbatuwar wannan nasarar za ta dora Birtaniya kan turbar barin kungiyar Tarayar Turai a watan Janairun shekara mai kamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI