Lebanon

Yan Sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Lebanon

'Yan sanda kwantar da tarzoma na kokarin tarwatsa masu zanga - zanga a Beyrouht na kasar Lebanon
'Yan sanda kwantar da tarzoma na kokarin tarwatsa masu zanga - zanga a Beyrouht na kasar Lebanon RFI

Arrangama ta kaure tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga a Beyrouth na kasar Lebanon.Masu zanga-zangar sun yi kokarin sa kai zuwa majalisar dokokin kasar, lamarin da ya kai jami’an tsaro ga yi amfani da barkonon tsofuwa domin tarwatsa duban masu zanga-zangar.

Talla

Yan siyasa sun kasa cimma daidaito domin fitar da sunanmutum daya da zai maye gurbin tsohon Firaminista Saad Hariri da yayi murabis.

Saad Hariri ne yanzu haka ake sa ran Shugaban kasar zai sake baiwa mukamin Firaminista,matakin da ga duk alamu masu zanga-zanga zasu yi adawa a kai.

Yan kasar na kallon tsohuwar gwamnatin Saad Hariri a matsayin gwamnatin da ta assasa cin hanci da rashawa, banda haka ta nuna gazawa a nauyin da aka dora mata.

Akalla mutane goma ne aka garzaya da su zuwa asibiti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI