Libya-Turkiya

Erdogan ya gana da Firaministan Libya

shugaban Turkiya, Recep Erdogan yayin ganawar sa da Firaministan Libya
shugaban Turkiya, Recep Erdogan yayin ganawar sa da Firaministan Libya Mustafa Kamaci / TURKISH PRESIDENTIAL PRESS SERVICE / AFP

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya gana da Firaministan Libya Fayez al-Sarraj a Santanbul, kwanaki bayan da shugaban yace a shirye yake ya tura da dakaru Libya idan kasar ta bukaci haka.

Talla

Babu dai cikkaken bayani kan ganawar da shugabannin biyu suka yi a asirce, amma a wata ganawa da suka yi ranar 27 ga watan Nuwamba, kasashen biyu sun amince da shirin hadin kan tsaro da na soji da kuma jiragen ruwa.

Turkiya da Qatar na goyawa gwamnatin rikon kwaryar Libya baya ne, yayin da kasashen Saudi Arabia da Masar da kuma Daular Larabawa ke goyan bayan Khalifa Haftar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.