Wasanni

A yau za a fitar da jadawalin gasar UEFA a birnin Nyon

Cibiyar hukumar kwallon kafa ta UEFA a Nyon dake kasar Swiziland
Cibiyar hukumar kwallon kafa ta UEFA a Nyon dake kasar Swiziland REUTERS/Denis Balibouse/File Photo

A yau za a fitar da jadawalin gasar cin kofin zakarun Turai na Uefa a birnin Nyon na kasar Swiziland .Kungiyoyi 16 ne suka rage ,da za mu iya zanawa kamar haka :A aji na farkoPSG, Bayern Munich, Manchesterd City, Juventus de Turin, Liverpool, Barcalona, RP Liepzig da Valence.A aji na biyu:Real Madrid, Tottenham, Atlhetico Madrid, Naples, Dortmund, Chelsea, Lyon, Atlanta Bergame.

Talla

Yayinda ake dakon jadawalin , wasu daga cikin masu horar da kungiyoyin kwallon kafa sun soma bayyana tsokacin su.

Zinedine Zidane mai horar da kungiyar kwallon kafar Real Madrid ya jaddada cewa mudin suka hadu da kungiyar Liverpool a Liverpool to ba wata tattanma za su lalasa kulob na Liverpool,mutumen da bai fida tsamanin sake shiga tarihi da kafar dama kamar dai yada Real Madrid ta yi a shekara ta 2018 tareda lashe kofin.

Real Madrid ta kasance ta biyu a fafatawar farko da kungiyoyin suka yi wanda ya kai ta ga wannan matsayi na samu tikitin shiga sahun kasashe 16 dake wannan mataki.

Kungiyar Real Madrid ce indan aka yi tuni ta lashe kofin a shekara ta 2016-2017 ka na 2018, inda ake kuma hasashen za ta iya shiga sahu na karshe domin haduwa ko fafatawa da kungiyoyi da suka hada da Juventus de Turin kungiyar Cristiano Ronaldo,ko Bayern Munich ko kuma Manchesterd City a karkashin Pep Guardiola.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.