Isa ga babban shafi
Turai

Yan Sanda sun tarwatsa masu neman afkawa Shugaba Macron

Masu zanga-zanga a kasar Faransa
Masu zanga-zanga a kasar Faransa REUTERS/Benoit Tessier
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 1

Wasu daga cikin masu bore sun yi kokarin kutsawa cikin wani gidan kalo da Emmanuel Macron Shugaban kasar da mai dakin sa suke ciki a birnin Paris na kasar Faransa a jiya juma'a.

Talla

Shugaban kasar da gwamnatin sa na fuskantar bore biyo bayan daukar wasu matakai na kawo gyara ga dokokin da suka jibanci ritaya a Faransa,lamarin da ya janyo yajin aiki ga wasu sassan masana’antu Faransa.

Yan Sanda da masu tsare Shugaban kasar sun samu nasarar kange masu bore,wanda Shugaban kasar yayi amfani da haka domin ficewa daga wannan wuri bisa rakiyar yan Sanda.

A Faransa duban ma’aikata ne ke cigaba da gudanar da yajin aiki domin nuna bacin ran su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.