Turai

Luxembourg ta zama kasa ta farko da ta mayar da sufuri kyauta

Daya daga cikin jiragen jigilar jama'a a Luxembourg
Daya daga cikin jiragen jigilar jama'a a Luxembourg JOHN THYS / AFP

Kasar Luxembourg ta zama kasar duniya ta farko da ta mayar da harkokin sufurin ta kyauta domin taimakawa ma’aikata da kuma marasa karfi.Wannan shiri da aka kaddamar zai taimaka wajen saukakewa akalla kashi 40 na al’ummar kasar wajen gudanar da zirga zirga da kuma hana su kashe akalla euro 100 wajen biyan kudin sufuri.

Talla

Hukumomin kasar sun ce matakin wani yunkuri ne na takaita yawan ababan hawan da jama’a ke amfani da su da kuma basu damar amfana da wannan shirin na tafiye tafiye kyauta.

Akalla ma’aikata sama da 200,000 dake zama a kasashen Faransa da Jamus da kuma Belgium ke amfani da motoci zuwa kasar, abinda ke haifar da matsalar cunkoson ababan hawa da kuma gurbata muhalli.

Ita dai kasar Luxembourg na da yawan jama’a 610,000, kuma tana daga cikin kasashe masu arziki a Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.