Bankin Duniya

Bankin duniya ya taimaka da kudi don yakar Cutar Coronavirus

Ganin yadda cutar coronavirus ke cigaba da yaduwa kasashe da dama da kuma haifar da asarar karin rayuka, Bankin Duniya ya sanar da bada agajin Dala biliyan 12 domin taimakawa kasashe yaki da ita.Shugaban Bankin David Malpass yace manufar bada wadannan kudade shine domin ganin an dauki matakan gaggauwa domin tinkarar matsalar a kasashen da cutar ta afkawa.

Wani sashen filin tashi da saukar jiragen sama a China
Wani sashen filin tashi da saukar jiragen sama a China REUTERS/Thomas Peter
Talla

Shugaban hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya Tedros Adhanom Gebreyesus yace ya zuwa yanzu cutar tafi yin illa a kasashe 3, yayin da ta shiga kasashen duniya da dama. Shugaban hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya y ace ya fahimci cewar mutane na fargaba tare da tababa, haka yake wajen fuskantar duk wata barazana, musamman idan barazana ce da bamu fahimce ta ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI